ASALIN KABILAR HAUSA
ASALIN KABILAR HAUSA DA KALMAR HAUSA
ASALIN HAUSAWA DA DANGINSU
kabilar hausa nadaga cikin kabilun bakaken Afirka 'ya'yan Zangiy kenan wanda ya rayu a Misira bayan ɗaukewar ruwan ɗufana.
Saboda haka asalin hausawa mazauna Misira ne waɗanda kuma suka rinka gudanar da harkokinsu acan, musamman noma, kiwo da kasuwanci.
Daga bisani sai wani yanki na tushen ƙkabilar Hausa ya taso izuwa garuwan Habasha musamman yankin Dahalak, wanda yake cikin kasar Eritrea ayau.
Shi wannan yanki na Dahalak har yanzu akwai hausawa masu yawa acikinsa, daga baya ne larabawa suka shiga suka zauna tare da hausawa a cikinsa.
An samu waɗansu mutane guda uku da suka fito daga waɗancan hausawa mazauna dahalak tare da iyalansu izuwa afirka ta yamma. Mutanen kuwa sune Dala, Rano, da Gaya...
MA'ANAR KALMAR HAUSA
ma'anar Hausa ta mabambantan fuskoki kamar yadda Ibrahim (1978) da Ɓaɓura (2008) suka kalle ta a matsayin kalma mai iya ɗaukar ma'anar harshe da mutanen da suke magana da harshen da kuma ƙasar da ake amfani da harshen. Bisa irin waɗannan bayanai ne aka ƙara da cewa: Hausa kalma ce mai faffaɗar ma'ana da take wakiltar Hausawa da harshensu da azancinsu da ƙasarsu da kuma nazarin al'amuransu. Wato kalma ce da ta ƙunshi mabambantan ma'anoni a ƙalla guda biyar masu alaƙa ta ƙut da ƙut da junansu, musamman ta fuskar jama'a da yaren da suke magana da shi a matsayin harshensu da dabarun sarrafa tunani cikin harshen nasu da ƙasar da suke tutixya da ita a matsayin mazauninsu na dindindin da harkar nazari a fagen ilimin harshe da adabi da al'adu na Hausawan a makarantu da kwalejoji da jami'o'i a faɗin duniya.
Mahimman Kalmomi: Bita; Hausa; al'umma; harshe; azanci; ƙasa; nazari; ƙarni na 21.
Comments
Post a Comment