BABBAN NI'IMAN DA ALLAH YAYI HAUSAWA

FALALAR DA ALLAH YAYI WA HAUSAWA A DUNIYA

"Idan kai Bahaushe ne da ba ka cika yin karatun litattafai ba, to yana da kyau ka sadaukar da minti biyar na rayuwarka kasan wanene kai"

Harshen hausa ya fito daga cikin dangin harsunan nan da ake kira "Afro Asiatic" ko kuma "Hemito-Semito" su hudu ne kawai a Duniya da akwai Hausa, Arabic, Hebrew (Yahudanci), Amharic. Idan baka sani ba harshen hausa ya fito daga dangin harsuna mafi girman tarihi da alfarma a duniya.

Sune mazauna yankin Arewacin Nijeriya, da kuma kudancin Nijar anan suka fi yawa amma ana samu su a yankunan ƙasashen Afrika da yawa, kamar Chad, Ghana, Sudan, Benin, Togo, Cameroon, Senegal, Eritrea, Mauritania, Libya, Gabon, Ivory coast, Burkina Faso dss.

Ana samun Hausawa a yankunan da bana Afrika ba, misali akwai hausawa sama da mutum miliyan guda a kasar Saudi Arabia. A yanzu haka harshen hausa official language ne da yana cikin harsunan da masarautar Saudiya ta amince a fassara huɗubobi da sauran abubuwan addini dashi.

Harshen Hausa shine harshen da ya fi kowa ne harshe yawan masu amfani dashi a Afrika, wato asalin masu harshen sun haura mutum miliyan 65 sannan sune suka fi kowane harshe yawan masu amfani da shi a Afrika da ya haura mutum miliyan 154.

Harsuna biyu ne kadai a Afrika sanannu a duniya. Na farko Hausa ne, sai kuman Swahili. Shi yasa za kaga kusan komai na duniya indai ana fasaara shi, to akwai na hausar shi da kuma Swahili wani lokacin, banda wadannan harsunan babu wasu kuma.

Hakan yasa kabilar hausa ta shiga cikin harsuna 10 da suka fi kowane harshe karfin fada aji a duniya, akwai harsuna a duniya sama da dubu bakwai da dari daya 7,100. Amma harshen Hausa ya samu matsayin shiga cikin 10 mafiya karfi. Nasan ba kowa yasan wannan ba.

Shine kadai harshen da ake koyarwa a jami'oin wasu kasashen da ba Nijeriya ba, akeyi Degree har Professor ake zama. Shi yasa za kaje kasar waje Turai kaga ance maka wannan Professor ne a Hausa, kuma bai ma taba zuwa arewacin Nijeriya ba. Kamar dai yadda ake iy

Comments

Popular posts from this blog

HAUSA ITACE KABILA MAFI GIRMA A AFRICA